Daga Ibrahim Sani Gama
Gamayyar kungiyoyin kasuwar robobi ta kofar wambai ta koka dangane da matakin da gwamnatin jihar kano ta dauka na rushe gine-ginen dake filin idi, da kuma, yadda wasu batagarin matasa suke kwashe kayayyakin al’umma a matsayin ganima.
“Kamata yayi gwamnati ta yi duba na tsanaki da tausayawa yan kasuwa a matsayinta ta uwar kowa, da aka zabe ta domin ta yi fafutukar samarwa al’ummar jihar kano aiyukan yi don inganta rayuwar su”.
Da dumi-dumi: Bola Tinubu ya Magantu kan rushe gine-gine da gwamnatin Abba Gida-gida ke yi a Kano
Shugaban kungiyar Shariff Sama’ila na Ta’ala ne, ya yi koken lokacin da gamayyar kungiyoyin suka gudanar da taron manema labarai a kasuwar dake nan jihar kano.
Samaila Nata’ala, ya bayyana cewa, kananan ‘yan kasuwa da suka karbi hayar wuraren da take rusawa yanzu ta karya wasu da dama wadanda yanzu basu da tudun dafawa, sakamakon yadda aka hada da kayansu aka rushe da kuma wadanda bata gari suka kwasa da sunan ganima.
“Kamata yayi a rika baiwa mutane lokacin da za su rika kwashe kayayyansu domin kaucewa yin asarar da ba lallai ne su iya mayar da ita ba”. A cewar Sama’ila Nata’ala
Shugaban gamayyar kungiyoyin ya jaddada cewa, kungiyoyin a shirye suke idan gwamnatin jihar kano ta nemesu su zauna domin tattaunawa kan yadda za’a shawo kan matsalar dake tsakanin gwamnati da al’ummar da suka mallakin gurare a yankunan.
Haka zalika, yace kungiyoyin masu biyayya ne ga tsarin gwamnati, amma akwai bukatar yin duba na musamman akan lamarin nasu duba da asarar da sukai waccce har yanzu ba su kai ga tantance ta ba.