Sarkin Bichi ya jagoranci raba kekunan guragu na zamani a Masarautar

Date:

Daga Abubakar Lawan

Masarauta Bichi ta hadi gwiwar Kwamiti Matasa domin samar da Nigeria ta gari da kuma hukumar tace fina-finai ta kasa sun samar kekunan Guragu na zamani guda Ashiri ga guragun dake Kananan hukumomin tara dake Karkashin Masarauta .

 

A jawabinsa mai martaba Sarkin Bichi, yace an Samar da Sabbin kekunan ne domin saukaka masu bukata ta musamman, sannan yayi kira ga wadanda suka amfana da su yi amfani da kekunan yadda ya dace.

Sarkin ya kuma hori su da kada su siyar da kekunan domin kuwa Masarautltar za tasa ido sosai domin gani anyi abinda ya dace da kekunan.

Kwankwaso ya nemi kotu ta kawace Nasarar wani dan majalisar tarayyar NNPP a Kano

Alh Nasir Ado Bayero ya godewar Kwamiti na Matasa da kuma hukumar tace Fina-finai ta Kasa bisa kokarin da sukai na samar da abubuwan cigaba a Masarauta ta Bichi.

Da dumi-dumi: Bola Tinubu ya Magantu kan rushe gine-gine da gwamnatin Abba Gida-gida ke yi a Kano

A Jawabinsa Shugaban Kwamiti Matasa domin Nigeria tagari Alh. Ibrahim I Ibrahim yace sun yi kokarin Samar da kekunan hadi da Masarauta Bichi duba da kokari Mai Marbata Sarkin na Bichi Alh Nasir Ado Bayero, na kokarin kawo abubawan cigaba zuwa Masarauta ta Bichi.

Ya kuma tabbatarwa sarki cewa zasu cigaba da samar da abubuwan ga al’ummar Masarauta musamman masu bukutar ta musamman dama masu karamin karfi.

Mallam Shafi’u Yakubu daga Karamar hukumar Bagwai da kuma Mallama Hansa’u na daga cikin wadanda suka amfana sun yi godiya a madadi sauran sun godewa sarkin bisa wannnan talafi.

Taron rabon Kekunan ya sami halatar Kwamandar Sojoji Samar na Jahar Kano Air Command or G A Bello da Shugaban hukumar tace fina-fine ta Kasa Alh. Adebayo Thomas da kuma dukkan Hakimai Masarautar ta Bichi da sauran Jama’a da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...