Daga Rahama Umar Kwaru
A ranar Talata ne shugaban hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS) reshen jihar Ogun 1, Bamidele Makinde, ya tabbatar da sake bude iyakar Idiroko a jihar Ogun.
Makinde ya ce an sake bude iyakar tun shekarar da ta gabata, sabanin wani faifan bidiyo da ya nuna yadda wasu mazauna Idiroko ke murnar sake bude iyakar.
A watan Agustan 2019 ne tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rufe dukkan iyakokin kasa a wani bangare na kokarin dakile fasa kwauri da bunkasa noman shinkafa a cikin gida.
Janye tallafin mai: Gwamnonin jihohi na rage kwanakin aiki
A shekarar 2020, Buhari ya bayar da umarnin bude iyakokin a Seme a Legas, Illela a Sokoto, Maigatari a Jigawa, da Mfum a Cross River.
Kuma a cikin watan Afrilu, 2022, Buhari ya kuma ba da umarnin sake bude wasu kan iyakokin hudu da suka hada da Idiroko a Ogun, Jibiya a Katsina, Kamba a Kebbi da Ikom a Cross River.
Sai dai wani faifan bidiyo na dakika 21 da ke nuna yadda wasu jami’an hukumar kwastam ke gudanar da aikin sake bude kan iyakar Idiroko cikin farin ciki a ranar Litinin.
Da yake mayar da martani yayin ganawa da manema labarai a Abeokuta, Makinde ya ce tun wancan lokacin ne aka bude kan iyakar Idiroko sabanin yadda hoton bidiyo ya nuna.
Ya ce an bude iyakar Idiroko tare da Jibiya a Katsina, Kamba a Kebbi da kuma Ikom a Cross River.
Makinde, ya ce sauran iyakokin kasa a jihar kamar Imeko, Ohumbe, Ijofin da Ijoun na nan a rufe.
Ya ce, “A jihar Ogun, kamar yadda muke magana a yau muna da iyakokin da aka amince da su sama da shida, Imeko, Ijofin, Ijoun, Ohunbe, muna da shida daga cikinsu. Idiroko ne kawai aka bude yanzu, sauran suna nan a kulle.
“Yanzu, mun sami sabuwar gwamnati kuma mu ma’aikatan gwamnati ne kawai, muna aiwatar da manufofi da duk abin da gwamnatin ta ce muna yi.
“Don haka, Idiroko tana nan buɗe 24/7, amma sauran, ba mu da ikon buɗe su. Idan ku ka shigo da kayan kasuwanci ta can dole zamu, za mu kwace kayanku.”