Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaban kasar Nigeria Bola Tinubu na ganawa da gwamnonin jihohin kasar 36 a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.
Wannan ce ganawar shugaban ta farko da ƙungiyar gwamnonin ƙasar ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq tun bayan hawansa karagar mulki a makon da ya gabata.
Janye tallafin mai: Gwamnonin jihohi na rage kwanakin aiki
To amma a ranar Juma’ar da ta gabata shugaban ƙasar ya gana da wasu gwamnoni a ƙarƙashin ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki
Daga cikin masu halartar ganawar akwai mataimakin shugaban ƙasar Sanata Kashim Shettima da sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, da sauran jami’ai.