Daga Rukayya Abdullahi Maida
Rahotanni daga karamar hukumar Fagge da ke jihar Kano na nuni da cewa wasu matasa sun kewaye tsohon ginin kamfanin jaridar Triumph inda aka gina rukunin shaguna na zamani masu hawa uku suna kokarin kwashe kayayyakin dake ciki.
wasu ganau sun tabbatarwa kadaura24 cewa masu kwangilar aikin sun shiga ciki da mota domin kwashe wasu kayayyaki bayan wasika da ake zargin an rubuta kan rushe ginin.
Duk da cewa an girke Jami’an tsaro a kofar shiga, matasan sun balle kofar bayan ginin tare da fara cire kifofi da tagogi.
Ya zuwa yanzu dai matasan sun kwashe mafi yawa daga cikin kayan da aka Sanya a cikin gini duba da yadda matasan suka rika debo kaya irin su kofa tagogi, Kwanon rufi da ma rodikan da akai amfani da su wajen ginin .
KAYYASA! Hotunan yadda Abba Gida-gida ya rushe Daula otel da na Hajj Camp
Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta fara rushe wadansu gine-gine a jihar, Inda a yau Lahadi aka wayi gari da rushe ginin tsohuwar Daula Otel da wasu gine-gene dake filin sansanin alhazai
Ga wasu daga cikin hotunan yadda matasan suka yi sabon ginin.