Ba za mu lamunci afkawa kayan al’umma da sunan ganima ba – Abba Gida-gida

Date:

Daga Maryam Ibrahim Muhammad

 

Gwamnatin Jihar Kano na sanar da al’ummar Jihar cewa ba za ta lamunci afka wa gine-ginen mutane da sunan cin ganima ba, a dukkan sassan jihar.

Hotuna: Wasu matasa sun farwa sabbin shagunan tsohuwar Triumph dake Fagge

Haka kuma gwamnati na bayyana takaicin ta bisa yadda wasu Matasa suka afka wa ginin dake cikin tsohon gidan jaridar Triump da ke Fagge alhalin wannan ginin baya cikin lissafin wuraren da za a rushe.

 

Wannan sanarwa ce da gargaΙ—i daga ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi.

Sabo da haka gwamnatin na Ζ™ara jadadda cewar duk wanda aka samu da laifin afka wa wani gini tare da kwashe kayayyakin jikin sa zai gamu da fushin hukuma.

 

Gwamnatin ta Ζ™udiri aniyar yin aiki ne domin ci gaban Jihar Kano ba domin bai wa wasu lasisin rushe gine-gine da sace kayan mutane babu gaira babu dalili ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related