Hotuna: Wasu matasa sun farwa sabbin shagunan tsohuwar Triumph dake Fagge

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Rahotanni daga karamar hukumar Fagge da ke jihar Kano na nuni da cewa wasu matasa sun kewaye tsohon ginin kamfanin jaridar Triumph inda aka gina rukunin shaguna na zamani masu hawa uku suna kokarin kwashe kayayyakin dake ciki.

wasu ganau sun tabbatarwa kadaura24 cewa masu kwangilar aikin sun shiga ciki da mota domin kwashe wasu kayayyaki bayan wasika da ake zargin an rubuta kan rushe ginin.

 

Duk da cewa an girke Jami’an tsaro a kofar shiga, matasan sun balle kofar bayan ginin tare da fara cire kifofi da tagogi.

Ya zuwa yanzu dai matasan sun kwashe mafi yawa daga cikin kayan da aka Sanya a cikin gini duba da yadda matasan suka rika debo kaya irin su kofa tagogi, Kwanon rufi da ma rodikan da akai amfani da su wajen ginin .

KAYYASA! Hotunan yadda Abba Gida-gida ya rushe Daula otel da na Hajj Camp

Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta fara rushe wadansu gine-gine a jihar, Inda a yau Lahadi aka wayi gari da rushe ginin tsohuwar Daula Otel da  wasu gine-gene dake filin sansanin alhazai

Ga wasu daga cikin hotunan yadda matasan suka yi sabon ginin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...