Daga Kamal Yahaya Zakaria
Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin a gaggauta kwashe Sharar da suka cushe wasu titunan birnin Kano.
Idan za’a iya tunawa gwamna Abba Gida-gida ya kafa wani kwamiti mai suna NAZAFA wanda ya haka da dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar don magance matsalolin ambaliyar ruwa.
Hakan na cikin sanarwar da Sakataren yaɗa labaransa Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aike wa kadaura24.
Sanarwar ta ce taruwar Bola a kan tituna na nuna barazanar afkuwar ambaliyar ruwa.
“Ya zamar mana dole mu yo hayar motocin tifa domin kwashe tarin sharar da ake da ita a Kano , saboda hukumar REMASAB a yanzu bata da isassun motoci da kayan aikin da zata iya kwashe duk sharar da ake da ita a jihar kano”. Inji Abba Gida-gida
Sanarwar tace Gwamnan ya zargi tsohon gwamnan kano Ganduje da sayar da motocin kware shara da hukumar kware shara ta Kano take da su da sauran kayan aikin hukumar, Inda aka fake da hadin gwiwa da wani kamfanin yan kasuwa.