Daga Zakaria Adam Jigirya
Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji Abdulmumini Jibril Kofa ya mika sakon taya murna ga Shugaban majalisar wakilai Femi Bjabiamila saboda mikamin Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa wanda Shugaban kasa Bola Tinubu ya bashi.
” A madadin ni kaina da iyali na da duk mutanen Kiru da Bebeji da ma daukacin mutanen Nigeria Muna taya ka murnar wannan babban mukami da shugaban kasa ya baka ya baka”.

Kadaura24 ta rawaito Abdulmumini kofa ya bayyana sakon taya murnar ne cikin wata da ya wallafa a Sashin Shafinsa na Facebook.
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya Koka da yadda Ganduje ya bar masa bashi Mai tarin yawa
“Bamu yi mamakin wannan mukami da aka bashi ba saboda irin matakan ya taka da mukaman da ya rike a majalisar wakilai ta 7 da 8 na shugaban masu rinjaye Kuma ya zama Shugaban majalisa ta 9, wanann ya nuna cewa ya samu gogewar da zai iya rike wannan babban mukami da shugaban kasa ya bashi saboda gogewar sa”. A cewar Kofa
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Abba Gida-gida ya yi Sabbin nada-naden mukamai
Abdulmumini kofa yace suna kyautata zaton Femi Bjabiamila zai zama Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa na farko da ba’a taba yin irinsa ba Saboda gogewarsa da Kuma ba zai baiwa Shugaban kasa Bola Tinubu Kunya ba.
Kofa ya yi addu’ar Allah ya yi riko da hannun sabon shugaban ma’aikatan ya bashi ikon sauke nauyin da shugaban kasa ya dora masa.