Daga Sani Idris Maiwaya
Gwamnan Kano mai jiran gado Abba Kabir Yusuf ya ayyana kaɗarorin da ya mallaka ga hukumar ɗa’ar ma’aikata.
Sanarwar da ofishin gwamnan mai jiran gado ya fitar a ranar Juma’a ta ce Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kansa ga ofishin hukumar ɗa’ar ma’aikata da ke Kano tare da miƙa fom da ya cike na ƙadarorinsa.
“Na cika sharuɗɗan da kundin tsarin mulki ya gindaya na ayyana ƙadarorin da na mallaka kafin rantsar da ni a 29 ga Mayu,” in ji sanarwar.
Gobara ta tashi a Gidan da Ganduje ya Koma makonni biyu da suka gabata
Abba Kabir Yusuf ya kuma sanar da matakin a shafinsa na Twitter
Gwamnan mai jiran gado ya kuma bayyana cewa dukkanin jami’an da za su yi aiki a gwamnatinsa da suka ƙunshi har da muƙaman siyasa sai sun bayyana ƙadarorinsu kamar yadda doka ta tanada.
A ranar Litinin 29 ga Mayu za a rantsar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin sabon gwamnan Kano.