Akwai masu shirin tayar da hatsaniya a lokacin rantsar da sabbin gwamnatoci a Najeria – DSS

Date:

Daga Safiyanu Dantala Jobawa

 

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta bayyana cewa akwai wasu da suke shirin tayar da zaune tsaye a lokacin bukukuwan mika mulki da za a yi a wasu jihohin kasar a ranar 29 ga watan mayu.

 

A sanarwar da kakakin Hukumar DSS, Peter Afunanya ya fitar, hukumar ta bukaci jama’a da ƴan jarida da ƴan kungiyoyin farar hula da duk wasu masu ruwa da tsaki a harkar da su bi ka’idojin da aka tsara a lokacin bikin a ko’ina a fadin kasar.

Gwamnati tarayya ta amince bankuna su yi katin ATM mai hade da katin ɗan-ƙasa

A wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, hukumar DSS ta ce mutanen suna son yi wa aikin jami’an tsaro nakasu ne tare kuma da tayar da hankalin jama’a su jefa tsoro ga ‘yan kasar a lokacin.

Da dumi-dumi: Ganduje ya mika muhimman bayanan gwamnatin Kano ga Abba Gida-gida

Haka kuma sanarwar ta shawarci jama’a da su yi watsi da labaran karya ko na kanzon-kurege da na zuzuta al’amura da kuma duk wani abu na neman razanarwa.

Hukumar ta kuma shawarci duk wani mutum da ba shi da takardar izini ko ta tantancewa da ya kauce wa shiga wasu wuraren a lokacin da ake bikin.

DSSn ta bai wa jama’a tabbacin ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin ganin bukukuwan sun wakana lami lafiya cikin nasara a ko’ina a fadin kasar.

A ranar Litinin 29 ga watan nan na Mayu 2023 ne za a yi bikin mika mulki da rantsar da sabon shugaban kasa a Abuja da kuma gwamnoni a wasu jihohin Najeriyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...