Daga Sani Idris Maiwaya
Gwamnatin jihar kano ta miƙa muhimman bayanan gwamnatin ga kwamitin karɓar mulki na jam’iyyar NNPP dake karkashin jagorancin Shugaban kwamitin Dr Abdullahi Baffa Bichi.
Sakataren gwamnatin jihar kano Alhaji Usman Alhaji wanda shi ne shugaban kwamitin miƙa mulki na jam’iyyar APC ne ya mika muhimman bayanan a madadin gwamnatin mai barin gado a gidan gwamnatin kano.
” Muna godiya ga wannan kwamiti na karɓar mulki bisa yadda suka bamu hadin kai har muka samu nasarar kammala aikin da aka dora mana, hakazalika muka godewa sakatariyar mu saboda yadda suka rika aiki ba dare ba rana wajen ganin sun kammala aikin”.
Ganduje ya bude Ofishin Yan Sanda na zamani irinsa na farko a Kano
Usman Alhaji yace sun Sami fahimta juna sosai wajen gudanar da aiki saboda dukkanin bangarorin magana suke ta yadda za’a ciyar da jihar kano Gaba.
A jawabinsa Shugaban kwamitin karɓar mulki na jam’iyyar NNPP Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya yaba kwamitin miƙa mulkin Saboda yadda suka gudanar da aikin tattara bayanan.
“Zamu je mu duba wadannan muhimman bayanai da muka karba sannan mu bada shawarwari ga sabon zaɓaɓɓen gwamnan kano Engr. Abba Kabir Yusuf domin duba yadda za’a inganta rayuwar al’ummar jihar kano”.
Wannan dai na daga cikin tsare-tsaren shigar sabuwar gwamnati domin kama aiki a ranar litinin mai zuwa 29 ga watan mayun wanann shekara.