Daga Sani Idris Maiwaya
kwamitin karbar mulki na gwamnan Kano mai jiran gado Abba Kabir Yusuf ya bukaci al’ummar jihar kano da su taimakawa gwamnati mai jira da bayanai game da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.
Shugaban kwamitin Dr. Baffa Bichi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikowa kadaura24.
Sanarwar ta nemi duk wanda ke da wasu muhimman bayanai kan yadda aka gudanar da gwamnatin Kano daga shekarar 2015 zuwa 2023, zai Iya mika bayanan shalkwatar kwamitin karbar mulkin dake Tahir Guest Palace, lamba. 4 Ibrahim Natsugunne Road.
Doguwa ya janye daga takarar shugabancin majalisa, zai marawa wani baya
“Haka kuma zai iya aike da bayanan ta wannan adireshin Gmail: GTC2023@gmail.com”. A cewar sanarwar
Wannan na zuwane yayin da ya rage kwanaki 11 a rantsar da sabuwar gwamnati a Kano da matakin Kasa baki daya.