Daga Rahama Umar Kwaru
Guda cikin dattawan kasar na Alhaji Isa Bello ja ya bukaci al’ummar Nigeria da su kyautata zato ga sabuwar gwamnati domin samun ingantacciyar rayuwa ga al’umma ƙasar nan baki daya.
” Babu shakka sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu yana da kwarewa a al’amuran da ya shafi Shugabanci, don haka muke yi masa kyakyawan zato”.
Alhaji Isa Bello Ja ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da jaridar kadaura24 a Kano.
Auren dole: Wata Matashiya ta yi karar Mahaifinta a kotu
” Ya yi Gwamnan Jihar Lagos kuma shi ya dora jihar a tafarki na cigaba har ta kai yadda take a halin yanzu, ya inganta tattalin arziki jihar fiye da na kowacce jiha a Nigeria, to haka muke tsammani zai yiwa Nigeria”. Inji Shi
Alhaji Isa Bello Ja wanda ake yi masa lakabi da Dattijon arziƙi yace yana da kwarin gwiwar matsalolin Nigeria zasu kadau idan al’ummar Nigeria suka dage da yiwa sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa addu’o’in samun nasara.