Daga Safiyanu Dantala Jobawa
Akwai yiwuwar za a karawa kowanne mahajjaci daga Nigeria kuɗin aikin Hajjin bana har akalla dala 250 sakamakon yaƙin dake faruwa a kasar Sudan.
Majiyar Kadaura24 Bizpoint ta rawaito cewa an dauki wannan matakin ne a wata yarjejeniya tsakanin hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON da kamfanonin jiragen sama da aka ware domin jigilar alhazan bana, wanda aka gudanar a Abuja ranar Talata.
An bayyana cewa, kamfanonin jiragen da suka hada da Max Air mai 16,326, Air Peace mai 11,348, Azman Air mai 8,660, da Aero Contractors 7,833, sun ki sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar 4 ga watan Mayu, har sai an warware batun biyan karin kudade saboda rikicin Sudan.
Majalisa ta 10: Yan Majalisun adawa sama da 183 sun fara yunkuri kafa Shugabancin majalisar
Majiyoyin cikin gida sun shaidawa manema labarai cewa an dauki matakin ne saboda muradun bangarorin biyu don hana kamfanonin jiragen sama yin asara sakamakon rufe sararin samaniyar Sudan sakamakon rikicin da ake fama da shi a kasar.
Kwacen waya: ‘Yan Sanda a kano sun kama matasa 27
Kamfanonin jiragen za su bi ta wata hanya wacce daga dukkan alamu ta fi tsawan awanni uku a kalla za ta bi ta Sudan.
Dangane da haka, a cewar majiyar, a yayin da aka sake zama taron a yau, an amince gaba daya cewa za a kara dala 250 ga kowane mahajjaci.
“Saboda wannan rikici a Sudan, wanda ya tilastawa kasar rufe sararin samaniya, an tsawaita tafiya Saudiyya daga Najeriya da akalla sa’o’i uku.
“Dole ne mu bi wasu hanyoyi; dole ne ku ratsa sama da kasashe biyar, wanda hakan ya sa tafiyar ta kara tsayi. Kuma duk kasar da za ka wuce, sai ka biya kudin amfani da sararin samaniyarta.
“Saboda haka, an amince a yau cewa za a kara dala 250 a kan kowane mahajjaci,” in ji majiyar.
Majiyar ta kara da cewa NAHCON, wacce ta bayyana hakan, ba ta bayyana wanda zai biya karin kudin jigilar maniyyatan ba ko gwamnati ko Kuma su mahajjatan.
Sai dai majiyoyin sun bayyana cewa a cikin yarjejeniyar an amince da cewa idan al’amura suka dawo a Sudan kuma aka bude sararin samaniyar kafin a fara jigilar to za’a dakatar da biyan dalar Amurka $250 din.