Mun magance kisan yan kungiyar masu fataucin shanu a Nigeria – Mustapha Ali

Date:

Daga Ibrahim Sani Gama

Kungiyar masu fataucin shanu da Dabbobi ta kasa,ta bayyana cewa, ta bijiro da shirye-shirye domin inganta harkokin safarar shanu da Dabbobi zuwa kudancin kasar nan.

Shugaban kungiyar masu fataucin shanun na kasa Mustapha Ali ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a jihar kano.

Mustapha Ali yace a lokutan baya duk dan kungiyar da zai yi safarar shanu da dabbobi zuwa jihohin kuduncin Nigeria, sai ya rike kudade wajen dubu Dari domin baiwa wasu mutane ba gaira ba dalili.

Yakin Sudan: Mun yi Nasarar Kwaso duk ‘Yan Nijeriya Da Suka Makale A Khartoum -Gwamnatin tarayya

” Mun taka muhimmiyar rawa wajen dakatar da hakan kisan mambobinmu wanda bai kamata haka ta rika faruwa ba, wannan na daga cikin nasarorin da kungiyar ta samu”. Inji Mustapha

“Idan ya’yan kungiyar mu sun mutu muka taimakawa iyalansu musamman a lokutan  karamar salla da Babba “.

Me ke Shirin faruwa tsakanin Stephanie da Nasir Danmalan na Shirin Dadin kowa ?

Shugaban kungiyar masu fataucin shanu da Dabbobi ya bayyana cewa, yana fatan Gwamnati mai jiran gado karkashin Shugabancin Bola Ahmed Tunubu, za ta kawowa kungiyar dauki da bata damar da ta kamata domin bunkasa harkokin yan kungiyar a kasa baki daya.

Shugaban ya kuma yace kungiyar za ta ci gaba da baiwa Gwamnati cikakken hadin kan daya dace,musamman wajen samarwa matasa ayyukan yi da biyan Gwamnati kudaden haraji domin ciyar da kasar nan gaba ta yadda za ta bijiro da managartan ayyukan ci gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...