Yakin Sudan: Mun yi Nasarar Kwaso duk ‘Yan Nijeriya Da Suka Makale A Khartoum – Gwamnatin tarayya

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin tarayya ta ce ta samu nasarar kwashe dukkan ‘yan Najeriya da suka makale a birnin Khartoum na kasar Sudan mai fama da rikici.

Dokta Sani Gwarzo, babban sakatare a ma’aikatar jin kai ta tarayya ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi kashin na biyu na mutane 130 da aka kwaso a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Da dumi-dumi: Yan Sanda a kano sun kama matashin da ya kashe mahaifiyarsa da wuka

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa mutanen sun isa tashar Alhazai ta filin jirgin da misalin karfe 3:10 na rana a cikin jirgin TARCO Aircraft Mai lamba B373-300 daga Port Sudan.

Kwamitin Baffa Bichi bashi da ikon kiran manyan Sakatarorin gwamnatin Kano – Kwankwaso

“Ina mai farin cikin sanar da cewa, mun yi nasarar dauko duk wanda ya bukaci a dauko shi daga Khartoum, babu wani abokin aikin ku a yau a Khartoum, duk sun bar garin.

“Ku ne rukunin farko da kuka tashi daga Khartoum zuwa iyakar Masar, har yanzu muna da kadan daga cikinku, yayin da wasu kuma tuni suka isa Najeriya.

“Ko da yake mafi yawansu za su iso nan da sa’o’i takwas ko sama da haka, don haka a lokacin, da babu wani dan Najeriya da aka bari a kan iyakar Masar,” in ji Gwarzo.

Ya ce tuni kaso na biyu sun tasovta jirgin sama daga Port Sudan.

“Amma mun yi isassun shirye-shirye don jigilar dawo da sauran wadanda suka rage cikin ‘yan kwanaki masu zuwa. Muna da kusan mutane 1,700 a can kuma mun yi isassun shirye-shiryen jiragen da za su dawo da su gida. Labari mai dadi shi ne babu wani rai da aka rasa acan ,” inji shi.

Gwarzo ya ce a cikin mutane 130 da aka kwaso maza 2 ne kawai yayin da sauran duk mata da kananan yara ne .

Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa tawagar za ta ci gaba da baiwa mata da yara da kuma marasa lafiya a cikin su fifiko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...