Daga Safiyanu Dantala Jobawa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake bayyana jin dadinsa da yadda zaben 2023 ya gudana a Najeriya, duba da yadda aka samu fitowar masu zabe da kuma yanayin zaman lafiya da aka samu yayin zaɓen .
Shugaban wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga takwarorinsa a taron shugabannin kasashe rainon ingila wato Commonwealth wanda aka gudanar a ranar Juma’a a birnin Landan, ya ce kasar ta koyi darasi da zai sa zabubbukan da za’a gudanar nan su kara inganta.
Da dumi-dumi: Yan Sanda a kano sun kama matashin da ya kashe mahaifiyarsa da wuka
A Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya fitar ranar Juma’a a Abuja, ya ce taron na daga cikin manyan al’amuran da aka tsara gabanin bikin nadin sarautar mai martaba, Sarki Charles III a matsayin Sarkin Birtaniya kuma shugaban kungiyar kasashe rainon ingila.
Me ke Shirin faruwa tsakanin Stephanie da Nasir Danmalan na Shirin Dadin kowa ?
Shugaban na Najeriya ya ce: “ An sami fitowar masu zabe a Wadancan zabukan da suka gabata sannan kuma an tabbatar da cewa dimokuradiyyar Najeriya ta kara girma.
“Duk da matsalolin na rikici da aka samu a wasu sassa na kasar, amma mun nuna cewa gwamnati zata iya gudanar da zabe cikin lumana da adalci.