Yan Sanda a Kano na neman matashin da ya kashe mahaifiyarsa ruwa a jallo

Date:

Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kano ta ce tana neman wani matashi ruwa a jallo, wanda ake zargi da caccaka wa mahaifiyarsa wuƙa a kanta da ƙirjinta da sauran sassan jiki.

Da yake tattaunawa da BBC, kakakin ‘yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce matashin mai shekara 22, ya tsere bayan caccaka wa mahaifiyar tasa mai shekara 50 wuƙa.

Da dumi-dumi: Allah kadai yasan jam’iyyar da zan mikawa mulkin Kano – Ganduje

Ya ce ‘yan sanda sun yi nasarar gano wuƙar da aka yi aika-aikar da ita a unguwar Rimin Keɓe da ke wajen birnin Kano.

Da yammacin ranar Laraba ne matashin da ake zargi ya aikata kisan kan ga mahaifiyarsa wadda a yanzu ba sa tare da mahaifin nasa.

A cewarsa, tuni sun baza koma inda suke ci gaba da neman matashin domin kama shi.

“Mutane na ci gaba da yaɗa cewa an taɓa kai shi (asibitin masu taɓin hankali da ke) Dawanau, amma dai mu muna ci gaba da aikinmu,” in ji SP Abdullahi Kiyawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...