Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli ta lashe gasar lig ta Serie A ta ƙasar Italiya.

Karon farko cikin shekara 33, rabon da ta ci kofin, tun lokacin Maradona ya na kyaftin ɗinta.
Me ke Shirin faruwa tsakanin Stephanie da Nasir Danmalan na Shirin Dadin kowa ?
Nasrar na zuwa ne bayan canjaras da ta yi da Udinese a gidanta 1-1.
Ɗan wasan gabanta da ya fi haskakawa a wannan shekarar Victor Osimhen ya farke kwallon da aka fara jefa mata.