Daga Sani Idris Maiwaya
Zababben Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya taya ma’aikatan gwamnati dana kamfanoni masu zaman kansu dake jihar murnar zagayowar ranar ma’aikata ta 2023.
Zababben Gwamnan ya ajiye aikin gwamnati sama da shekaru 10 da suka gabata, Inda ya yi aiki sama da shekaru 20 a wurare daban-daban a bangaren ruwa na jihar kano .
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran zaɓaɓɓen gwamnan kano Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Masarautun kano 5 nan gani nan bari – Gwamna Ganduje
Ya ce ma’aikata su ne jigon samar da shugabanci nagari a duk wani tsarin dimokuradiyya, don haka sun cancanci a yaba musu bisa sadaukarwar da suke yi wajen gudanar da aikin su.
Engr. Abba Kabir Yusuf ya baiwa ma’aikatan jihar tabbacin samun Ingantacciyar walwala da suka hada da gaggauta biyan albashi da fansho daga gwamnatin jam’iyyar NNPP mai jiran gado.
Ma’aikata a Najeriya sun shiga halin kakanikayi lokacin mulkin Buhari – NLC
Engr. Abba ya ce gwamnati mai jiran gado yana sane da matsalolin da ma’aikatan jihar ke fuskanta da suka hada da rashin kyawun yanayin aiki da rashin isassun ma’aikata da dai sauransu kuma za’a gyara su.
Ya ce gwamnatinsa za ta himmatu wajen gyara ma’aikatan gwamnati a wani bangare na kokarin karfafa tsarin samar da ayyuka masu inganci.
“Kamar yadda yake a cikin tsarin mu, za mu kafa Cibiyar Horar da Ma’aikatan Gwamnati don dacewa da mafi kyawun ayyuka na duniya.”
Dangane da yadda ake tafka ta’asa da nuna son kai a aikin daukar ma’aikata da gwamnatin mai barin gado ke aiwatarwa, zababben gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta sake duba duk wasu ayyukan da ba su dace ba tare da tabbatar da samar da sahihin tsarin daukar ma’aikata ga duk ‘yan jihar kano da suka cancantar shiga aikin gwamnati.