Ranar ma’aikata: Na inganta rayuwar ma’aikatan Kano fiye da na kowacce jiha a Nigeria – Ganduje

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi ya bayyana cewa a tsahon shekaru 8 da yayi a kujerar gwamnan jihar ya Kyautata rayuwar ma’aikatan ta fannoni daban-daban.

 

” A tsahon wannan shekaru babu wani ma’aikaci da ya ke bin na bashin koda sisin Kobo, duk da matsalolin tattalin arziΖ™in kasa da muka Rika fuskanta a tsahon shekaru 8″. Inji Ganduje

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wajen bikin ranar ma’aikata ta bana, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha dake kano.

Masarautun kano 5 nan gani nan bari – Gwamna Ganduje

Ganduje ya kuma bayyana cewa ya inganta aiyukan ma’aikata ta hanyar Samar da kyakyawan yanayi a ma’aikatunsa da Kuma yadda ya Rika biyan albashin ma’aikata da kudin wata-wata na yan fansho.

Ranar Ma’aikata: Zamu inganta rayuwar ma’aikatan gwamnati, ta Biyan Albashi da Fansho cikin gaggawa– Abba Gida-gida

” Bayan biyan hakkokin ma’aikata, mun Samar da gidaje masu sauΖ™i da Kuma Samar da basussuka masu sauΖ™i, tare da samar da tsarin taimakekeniya lafiya don Saukakawa musu da kuma kula da lafiyarsu”. A cewar Ganduje

 

Ganduje ya yabawa daukacin ma’aikatan kano bisa hadin kai da goyon baya da suka bashi tunda ya fara mulkin kano har ya kare ba tare da zanga-zanga ko yajin aiki ba.

A nasa jawabin shugaban kungiyar ma’aikatan jihar kano Kwamarat Kabiru Ado Inuwa ya yabawa gwamnan bisa yadda ya Kyautata rayuwar ma’aikatan jihar ta hanyar biyan hakkokin ma’aikata akan Kari.

Bayan ya bayyana nasarorin da kungiyar ta samu, Shugaban Yan Ζ™wadago ya kuma taya ma’aikatan jihar kano murnar zagayowar bikin wanann rana Mai muhimmanci ga ma’aikatan .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related