Daga Rabi’u Usman
Sama da Manoma 2000 ne suka gudanar da sallar alqunutu da Zanga-zangar lumana a garin Tamburawa dake kananan hukumomin Dawakin kudu, kumbotso da Madobi domin nuna damuwarsu kan zargin da suke yi wa gwamnatin Kano na kwace gonakinsu, da zummar za’ayi Masana’antu wanda akace za’ayi (Industrial area) a yankin garin na tamburawa.
Amma sai dai matsalar da suka ce suna fuskanta bata wuce rashin biyan su diyyar Gonakin su ba, suna masu cewar, sun bibiya Inda aka kwana game da batun biyan su hakkokin Gonakin su da aka karba? sai suka samu labari daga wasu mutane suna cewar, “duk wanda aka yiwa gonar sa kudi, babu shakka abin da za’a bashi bai wuce la’ada ba idan zai sayar da ita gonar tasa”.
Hakan ta sanya mutanen suka fito sukayi Sallar lqunuti domin neman mafita ga Ubangiji madaukakin Sarki da kuma nuna rashin amincewar su ga Mahukunta akan wannan matsalar da suke fuskanta.
Da dumi-dumi: Kwankwaso ya Magantu a kan batun dawo da Sarki Sunusi II Sarautar Kano
Jim kadan da idar da Sallar ne mutanen suka gudanar da zanga-zangar lumana a yankin, inda sukayi tattaki tun daga makarantar primary ta tamburawa zuwa Gonakin su, a nan ne suka yi zaman dabaro don gudun kar ma’aikatan ma’aikatar kasa da safayo ta jihar kano suyi musu abun da suka kirawo da aika- aika.
Mutanen dai suna dauke da kwalayen da aka rubuta :-
“Bamu yarda da zalunci ba”
“Bama Goyon Bayan kudirin gwamnati akan wannan yunkurin kwace mana Gona”
“Muma ‘yan kasa ne kamar kowa”
“Bazamu bari a kwace mana Gonakin mu ba”
Malam Muhammad Auwal shi ne limamin garin Matage dake karamar hukumar Dawakin Kudu, ya zargi shugaban karamar hukumar tasu da yin sama da fadi da gonar sa wadda aka yanka fuloti mai fadin kafa 50 har guda 12, wanda kudin kowanne fuloti ya tasamma naira dubu dari tara zuwa miliyan daya.
” A labarin da muka samu ance wai shugaban karamar hukumar Dawakin Kudun yace wai za’a kara girman garin ne, shiyasa ake bin masu gona dasu sayar ko kuma a biya su diyya a karbi Gonar tasu”. A cewar limamin
Shi ma Malam Isa yana daga cikin mutanen da aka auna gonar sa, har gonar tasa akayi kiyasin za’a biya shi naira miliyan dari, daga bisani aka ce sai dai ya yi hakuri za’a bashi naira miliyan tamanin, aka sake saukowa kasa akace za’a bashi naira miliyan Ashirin da bakwai, a karshe sai akace sai dai a bashi naira Dubu dari takwas.
Mutanen garuruwan da suka hadar da Matage, Tafki, Galinja, Kumbotso, Tamburawa, Magami, Kaba, Tudun Bayero, Garu, Tsamawa, Hausawa da sauran garuruwan, sun bayyana rashin jin dadin sa da kuma rashin amincewar su na kokarin gwamnatin kano akan wannan Masana’antar da za’ayi.
Jin hakan ne ta sanya muka kira Jami’in hulda da Jama’a na hukumar kasa da safayo ta jihar kano domin jin yadda akai aka haihu a ragaya, sau dai yace mu samu lokaci muje da wadannan mutane domin su tattauna akan idanun mu.
Shi ma Slshugaban karamar Hukumar Dawakin Kudu Hon Nasir Ibrahim Matage akan wannan korafi amma bai dauki waya ba, sai muka tura masa sakon kar ta kwana, kawo yanzu dai bamu samu ji daga Gare shi ba.
Da Zarar ya magantu zaku jimu dauke da karin bayani.