Rukunin farko na daliban Najeriya da aka kwashe daga kasar Sudan sun isa kan iyakar Aswan na kasar Masar a ranar Alhamis 27 ga watan Afrilu.
Shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM) Abike Dabiri-Erewa ta bayyana hakan a shafinta na Twitter a daren Alhamis.
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya halarci Faretin Sojoji Sanye da kakin Soji
Rukunin farkon sun isa kan iyakar Aswan ta ƙasar Masar, amma an riga an rufe iyakar a lokacin da suka Isa, amma a su tashi da sassafe sannan su wuce filin jirgin sama,” in ji abike
Yakin Sudan: An kaiwa daliban Nigeria hari
Hakazalika, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa ta ce rukunin farko na ‘yan Najeriya daga Sudan sun riga sun isa iyakar kasar Masar kuma za a kawo su Najeriya a yau Juma’a.
Mataimaki na musamman ga Darakta Janar na NEMA, Idris Muhammad, a ranar Juma’a ta gidan talabijin na Channels, Sunrise Daily, ya tabbatar da isowar rukunin farko na ‘yan Najeriya a kan iyakar ta Masar.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa wasu daga cikin daliban Najeriya sun kokan kan yadda aka bar su cikin mawuyacin hali a Sahara a jiya Alhamis.