Daga Auwalu Alhassan Kademi
Majalisar kula da tattalin arziƙin Najeriya ta ce ba yanzu ne lokacin da ya dace a cire tallafin man fetur ba a ƙasar.
Ministar Kuɗi da tsare-tsare ta ƙasa Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan bayan kammala taron Majalisar da aka yi a ranar Alhamis, wanda mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar gwamnati.
Ta ce za a ci gaba da dukkan ayyukan da aka fara game da shirin cire tallafin na tuntubar jihohi da sauran masu ruwa da tsaki, ciki har da wakilan sabuwar gwamnati mai jiran gado.
Yakin neman zabe: APC ta soke zuwan Tinubu Kano
“Majalisar ta amince da cewa dole ne a cire tallafi na farko cikin gaggawa ba tare da wani ɓata lokaci ba, domin kuwa ba abu ne mai ɗorewa ba”. A cewar Zainab shamsuna
“Ba za mu iya ci gaba da biya ba. Dole mu kalli yadda cire tallafin ba zai jefa rayuwar ‘yan Najeriya ba cikin mawuyacin hali.
“Akwai buƙatar neman mafita bayan cire tallafin muna buƙatar yin shiri game da hakan domin tabbatar da an taimaka wa mutane da cire tallafin zai shafa.”
Gwamnatin Najeriya ta ce ta karɓo aron dalar Amurka miliyan 800 daga Bankin Duniya domin sassauta wa mutane raɗaɗin cire tallafin.