Daga Sani Idris Maiwaya
Zababben Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya taya al’ummar musulmi da al’ummar Kano murnar kammala azumin watan Ramadan.
” Ramadan ya zo karshe sakamakon ganin jinjirin watan Shawwal, an koyi darussa na tausayi, karamci, taimakekeniya, zaman lafiya don haka ya kamata al’umma su dore da wadannan dabi’u don cigaban al’umma .
Sallah: NUJ reshen Kano ta bukaci zababbun shugabannin su magance kalubalen da kasar nan ke fuskanta
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu ranar Juma’a, zababben gwamnan jihar ya yi wa al’umma fatan alheri tare da gargadin jama’ar Kano da su yi addu’ar Allah ya baiwa shugabanni a dukkan matakai damar gudanar da aiyukan da al’umma zasu amfana.
Engr. Abba ya ce za’a yanayi Mai kyau nana gaba ga mutanen jihar kano, saboda gwamnati mai zuwa a karkashin sa za ta samar da yanayin siyasa mai kyau ga kowa ya zauna lafiya da kwanciyar hankali.
Ya bukaci ‘yan kasa da su kasance masu kishin kasa, masu son zaman lafiya tare da yin addu’ar samun zaman lafiya da ci gaban Kano da Nijeriya baki daya.
Abba Kabir Yusuf ya kuma yi gargadin a guji tukin ganganci yayin bukukuwan Sallah saboda hakan illa ce ga al’ummar jihar kano.