Tinubu ba ya bukatar kaso 25% na kuri’un FCT domin ya ci zaben Shugaban Kasa- INEC

Date:

Daga Umar Ibrahim Sani mainagge

 

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta shaida wa kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa cewa, zababben shugaban kasa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC, ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu kuma an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara ba tare da bukatar samun kashi 25 na kuri’un da aka kada ba Babban Birnin Tarayya Abuja ba .

 

INEC ta bayyana haka ne a martanin da lauyanta, Abubakar Mahmoud, ya bayar kan karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar suka shigar a gaban kotun.

 

Rashin wuta: ‘Yan KEDCO ya kamata ku nemi aljannar ku a wanann wata na Ramadan – Falakin Shinkafi

Ya ce dan takarar APCn ya cika dukkan sharuddan da doka ta tanada don bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, yana mai cewa ba dole ne dan takara ya samu kashi 25 cikin 100 na kuri’u a babban birnin tarayya Abuja ba domin kundin tsarin nigeria bai mai baiwa Abuja wani matsayi na musamman ba, kamar yadda wasu jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu suke fada wanda wannan kuskurene”.

Yan mata sama da dubu 42 ne suka daina zuwa makaranta saboda sun yin ciki – Rahoto

 

Akan dalilin da ya sa ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben kuwa, INEC ta ce dan takarar APC ya samu kashi 25 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada a jihohi 29 na tarayya Nigeria.

 

Haka kuma ta yi nuni da cewa bayyana Tinubu ba bisa kuskure ne ba ne kuma an yi shi ne bisa tanadin sashe na 134 (2) (b) na kundin tsarin mulkin kasar, inda ya samu kashi daya cikin hudu (25%) na sahihin kuri’un da aka kada. a jihohi 29 da suka wuce matakin da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

 

“Wanda ake kara na farko ya musanta cewa samun kashi 25 cikin 100 na kuri’un da aka kada a babban birnin tarayya, sharadi ne na bayyana dan takara a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa”.

 

Atiku Abubakar da PDP suna zargin cewa Tinubu bai sami mafi yawan kuri’un da aka kada a lokacin zaben ba kuma INEC ta karya ka’idojinta da tanadin dokar zabe, 2022 wajen gudanar da zaben.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...