‘Yan mata sama da dubu 42 ne suka daina zuwa makaranta saboda sun yin ciki – Rahoto

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

Kimanin ‘yan mata ‘yan makaranta 42,954 ne suka bar zuwa makaranta tsakanin Yuli 2021 da Yuni 2022 bayan sun sami juna biyu.

 

Wannan dai na zuwa ne a wani sabon rahoto da babban mai binciken kudi na kasar Tanzaniya (CAG) ya fitar ranar Litinin.

Likitoci a Najeriya sun soki sabon ƙudurin Majalisar wakila ta ƙasa

 

Rahoton CAG na shekarar 2021 zuwa 2022 da aka gabatar a majalisar dokokin kasar a Dodoma babban birnin kasar, ya ce daga cikin ‘yan mata 42,954 da ke da ciki, 23,009 sun fito daga makarantun sakandare, 19,945 kuma sun fito daga makarantun firamare.

An haramtawa limamai karanta Qur’ani daga wayar hannu a lokacin Tarawi da Tahajjud

 

Rahoton ya ce ‘yan matan sakandare da sukai yi ciki sun kai kashi 28 cikin 100 na ‘yan mata 82,236 da aka shirya zasu kammala karatunsu a shekarar 2021.

 

Rahoton ya ce, ga makarantun firamare, karamar hukumar Kwimba da ke yankin Mwanza ce ta fi kowacce yawan yara mata masu ciki a tsawon lokacin da akai bitar tare da ‘yan mata 9,045, sai kuma karamar hukumar Uvinza da ke yankin Kigoma da ke da ‘yan mata 2,172 suka yi ciki kamar yadda rahotan ya nuna. (NAN)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...