Likitoci a Najeriya sun soki sabon ƙudurin Majalisar wakila ta ƙasa

Date:

Daga Fatima Kabir Labaran

 

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya ta soki ƙudurin da majalisar wakilan ƙasar ta gabatar da ke neman tilasta wa likitoci aikin shekara biyar kafin samun lasisi.

 

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar bayan taron gaggawa na shugabannin kungiyar ta bayyana adawarta ga ƙudurin.

Buhari zai karkare fitar sa zuwa kasar waje a matsayin Shugaban Nigeria

Sanarwar ta ce ƙungiyar ta yi mamaki game da wanda ya gabatar da ƙudurin Hon. Ganiyu Johnson.

 

An haramtawa limamai karanta Qur’ani daga wayar hannu a lokacin Tarawi da Tahajjud

Haka kuma kungiyar ta bayyana damuwarta kan rashin biyan albashi da ta ce gwamnatin tarraya ba ta yi wasu daga cikin mambobinta, a yayin da wa’adin gwamnatin ke zuwa ƙarshe.

 

Ƙungiyar ta ce ta damu kan yunkurin majalisar wakilan na tilasta wa likitoci abin da ta kira da ”karin zangon shekara biyar bayan karatun digiri” kafin a ba su lasisi, ko a bar su su fita zuwa ƙasashen waje idan suna da sha’awar yin hakan.

 

Ƙungiyar ta kuma na nuna damuwa kan sake duba albashin mambobinta da ta ce gwamnatin tarayya ta gaza yi, duk kuwa da irin tarin alƙawuran da kungiyar ta ce gwamnatin ta sha yi musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...