Gidauniyar Bashariyya ta Tallafawa Marayu Sama da 50 da Kayan Sallah a Kano

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Gidauniyar Bashariyya foundation dake unguwar ‘yan tandu a karamar hukumar Dala ta tallafawa marayu da kayan abinchi da kayan sallah domin rage musu radadin halin maraici da suka tsinci kansu a ciki.

 

Shugaban kungiyar malam Bashir Aliyu yace suna gudanar da da rabon kayayyakin tallafin ne kimanin Shekaru hudu da suka gabata, domin tallafawa marayun dake unguwanni Adakawa ‘yan tandu domin ganin sun gudanar da Azumi da bukukuwan sallah cikin farin ciki da kwanciyar hankali.

 

Kimanin marayu 55 suka Amfana da tallafin kayan sallah , Sabulun wanka da kuma kayan Abinchi wanda gidauniyar ta raba musu domin rage musu radadi da kuma ganin ta taimakawa wadanda iyayen su suka rasu.

Ƙasar Ingila za ta dakatar da daukar ma’aikatan kiwon lafiya daga Najeriya

 

Malam Bashir Abubakar yace tallafawa marayu yana daga cikin ayyukan da Allah yake farin ciki . dashi hakanne yasa kungiyar take zage damtse wajan ganin ta gudanarda Rabon kayayyakin ga Marayun dake yankin.

 

Goman ƙarshe: Ya kamata matasa ku kashe Datar wayoyin ku, ku daina kallon TV – Dr. Ali Tamasi

Wasu daga cikin Marayun da. Suka amfana da tallafin Aisha sabiu da Jibrin Yahya sun bayyan farin cikinsu  dan gane da tallafin da aka basu

 

Wakilinmu Kamal Yakubu Ali ya bamu labarin cewa Taron ya gudana a farfajiyar makarantar dake unguwar yan tandu dake yankin karamar hukumar Dala.

 

Taron ya samu halarta iyayen. Marayu da kuma manayan unguwa da limamin masallacin Adakawa malam Nura Tahir da sauran alumma da dama. Da kuma Alhaji labaran sani Adakawa da kima Mai unguwar Adakawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...