Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi taβaziyya ga hamshakin dan kasuwar nan kuma dattijon Alhaji Aminu Alhassan Dantata CON da daukacin iyalan Dantata bisa rasuwar matarsa ββHajiya Rabi Aminu Alhassan Dantata.
Mai Martaba ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa mai tarin dukiya, kuma uwa mai tarbiyya wacce ta tsara rayuwar mutane da dama da ke kusa da ita ta yadda za su kasance masu inganci da adalci.
Goman Ζarshe: Ya kamata matasa ku kashe Datar wayoyin ku, ku daina kallon TV – Dr. Ali Tamasi
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24.
Sarkin wanda ya aika da tawaga karkashin Wazirin Kano Alhaji Saβadu Shehu Gidado yana mika taβaziyyarsa a madadin mai martaba Sarkin Kano da Majalisar Masarautar Kano da kuma alβummar Jihar Kano. Ya jajanta wa dattijon mai daraja, uba mai hangen nesa kuma mai fatan alherin samar da ci gaba, Alhaji Aminu Alhassan Dantata bisa rasuwar matarsa.
Ζasar Ingila za ta dakatar da daukar ma’aikatan kiwon lafiya daga Najeriya
Mai Martaba Sarkin, ya bayyana rasuwar Hajiya Rabi Aminu Dantata a matsayin babban rashi ba ga iyalanta da jihar Kano kadai ba, har ma ga sauran alβummar da kuma Najeriya baki daya.
Ya kuma yi adduβar Allah ya jikan marigayiyar yasa tana cikin Jannatul firdaus tare ya kuma bawa βyan uwa da iyalansa hakurin jure rashinta ya kuma ce wannan rashin wani babban rashi ne da ba za’a iya kwatantawa ba.
Sauran βyan tawagar sun hada da Walin Kano Alhaji Bashir Mahe Bashir da Dan Ruwatan Kano Alhaji Ibrahim Hamza Bayero da kuma sakataren mai martaba Sarki Alhaji Abdullahi Haruna Kwaru.
Da yake karbar tawagar a madadin iyalan Dantata, Alhaji Turado Dantata ya mika godiyarsa ga mai martaba Sarkin Kano bisa ziyarar taβaziyyar da ya kai masa, sannan ya kuma jajantawa sarkin bisa wannan banban rashi da akayi. Ya yi addu’ar Allah ya karawa jihar mu kano da Najeriya lafiya, zaman lafiya da kwanciyar hankali.