Daga Rukayya Abdullahi Maida
Hukumar kula da aikin hajji ta kasa Nahcon ta bayyana kudin kujerar aikin Hajj da maniyata ibadar aikin hajjin bana zasu biya domin sauke farali.
Shugaban Hukumar, Alhaji Zikirulla Kunle Hassan ne ya sanarwa manema labarai hakan, a yayin wani kwarkwaryar taron da hukumar ta gudanar da shugabannin hukumomin alhazai na jahohin Najeriya wanda ya gudana a ranar Juma’a.
Zikirulla yace karin kudin kujerar aikin Hajin na 2023 ya faru ne sakamakon tashin farashin canjin Dalar Amurka da kuma wasu inganta ayyukan kula da alhazai ta hukumomin Saudi Arabia suka yi.
Kammala zaben 2023: Abba Gida-gida ya baiwa shugabannin kananan hukumomin Kano shawara
Ya kuma sanar da ranar 21 ga watan Afurilu a matsayin rana ta karshe da hukumomin aikin hajji zasu sanyawa hukumar aikin hajin ta kasa kudaden Maniyyatan da zasu ta shi a jahohinsu ko kuma kamfanoninsu.
Da yake bayani dalla-dalla kan yadda biyan kudaden zai kasance tsakanin shiyyoyi ko jahohi a Najeriya, Zikirulla Kunle ya ce Jahohin dake yankin Arewa maniyyatansu zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da sha tara (2,900,19,000.00)
Kungiyar Ciyamomin kano ( ALGON) ta Gargadi Baffa Bichi kan shawarar da Abba Gida-gida ya ba su
Sai kuma maniyatan da zasu tashi ta Maiduguri da Yola, su kuma za su biya naira miliyan biyu da dubu dari takwas da casa’in ( 2,890,000.00). Yayin da jahar Edo zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da sittin da takwas (2,968,000.00). Sai Ekiti da Onda su kuma zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari takwas da tamanin (2,880,000.00)
Haka kuma jahohin Cross River da Osun zasu biya miliyan biyu da dubu dari tara da arba’in da takwas (2,943,000.000) da kuma miliyan biyu da dubu dari tara da casa’in da da uku (2,993,000.000)
Sai kuma jahohin Lagos da Ogun da Oyo, su kuma zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da casa’in da tara (2,999,000.000)
Sai yankunan Kudu masu Kudu da Kudu maso gabas, su kuma maniyyatansu zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da sittin da takwas (2,968,000.000)