Alhassan Ado Doguwa ya yi Nasara, Kotu ta bada umarnin karasa zaben Tudun Wada da Doguwa

Date:

Daga Abdulrashid B Imam

 

Kotun sauraren kararrakin zabe da ke zamanta a Kano ta ki amincewa da bukatar da Air Commodore Salisu Yusha’u (rtd) ya yi na neman kotun ta hana sake gudanar da zaben dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun-wada .

 

Tuni dai hukumar zabe mai zaman kanta ta sanya ranar 15 ga watan Afrilu domin kammala zaben da bai kammala ba a wasu yankin na yankin.

 

Kammala zaben 2023: Abba Gida-gida ya baiwa shugabannin kananan hukumomin Kano shawara

Mai shari’a L.B Lawal-Akapo, wanda ya jagoranci zaman kotun sauraron kararrakin zabe na Majalisar Dokoki ta Kasa da Jiha, ya ce kotun ba ta da hurumin dakatar da INEC daga karasa zabe a yankin.

 

Al’amarin dai ya biyo bayan hukuncin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yanke wanda tun da farko ta bayyana Alhassan Ado Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben, amma daga bisani ta bayyana cewa zaben bai kammala, kuma sakamakon farko an fade shi ne bisa tursasawa.

 

Kungiyar Ciyamomin kano ( ALGON) ta Gargadi Baffa Bichi kan shawarar da Abba Gida-gida ya ba su

Justice watch ta rawaito Lauyan mai kara, Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzirci ya garzaya kotu yana kalubalantar hukuncin da hukumar zabe mai zaman kanta ta yanke na ci gaba da shirin kammala zaben.

 

Lauyan ya kara da cewa dukkanin yan takarar kujerar a Doguwa da Tudun Wada sun ƙalubalanci matakin da hukumar ta dauka, Inda ya ce kotun tana da hurumin duba hukuncin da hukumar INEC ta yanke dangane da batun shirya sake zaben.

 

kotun dai ta yi watsi da bukatar dan takarar na NNPP sakamakon rashin hurumi rashin .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...