Zargin kisan kai: Ba da gangan aka jinkirta shari’ar Alhassan Ado Doguwa ba – Gwamnatin Kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani a kan zargin da wasu ke yi na cewa ta ƙi gurfanar da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta kasa Alhassan Ado Doguwa a gaban kotu.

 

Idan za’a iya tunawa ‘yan sanda sun kama Alhassan Ado Doguwa a ƙarshen watan Fabarairu, inda suka kai shi kotun majistare bisa zargin ya harbi wasu mutane, kwana ɗaya bayan zaɓen shugaban ƙasa a mazaɓarsa ta Doguwa/Tudun wada.

 

Sun kuma tuhumi ɗan majalisar wakilan da kashe mutum uku, da raunata wasu takwas a ƙaramar hukumar Doguwa lokacin da ake karɓar sakamakon zaɓe.

Direban jirgin sama ya yi artabu da maciji a kan kujerar zamansa a sararin samaniya

Kotun dai, ta ba da umarnin a tsare wanda ake zargin a gidan yari, kafin fara shari’a gadan-gadan.

 

Sai dai, kwana ɗaya kafin a mayar da shi kotun majistare, sai wata babbar kotun tarayya a Kano ta bayar da belin ɗan siyasar ranar 6 ga watan Maris.

 

Tun daga lokacin kuma ba a sake jin batun komawa don ci gaba da shari’ar ba.

El-Rufai ya mayar da malaman da ya kora bakin aiki

Lamarin dai ya sa ɓangarori da dama sun fara zargin ko hukumomi a Kano, na ƙoƙarin danne maganar, har ta bi ruwa.

 

To amma a martanin da ta mayar ranar Laraba, ma’aikatar shari’ar jihar Kano ta ce ba da gangan, ta ƙi kai shi kotu ba.

 

A cewarta, jinkirin da aka samu wajen ci gaba da shari’ar, wani al’amari ne, na ƙoƙarin bin tsari don tabbatar da adalci ga kowanne ɓangare.

 

BBC Hausa ta rawaito Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan ya ce tun lokacin da aka fara gabatar musu batun Alhassan Ado Doguwa, suka lura cewa akwai kura-kurai.

Aikin titin Abuja-Kaduna-Kano ba zai kammala a gwamnatin Buhari ba- Fashola

”Don kuwa akwai wasu batutuwa da ba a shigar da su cikin takardun da suka shafi zarge-zargen da ake yi wa ɗan siyasar ba,” in ji shi.

A cewar kwamishinan hakan zai iya kawo cikas a shari’ar, ko da an ci gaba da sauraren ta a kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...