Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Da tsakar ranar yau Laraba ne, akai jana’izar uwargidan tsohon gwamnan Kano, Hajiya Ladi Baƙo, bayan ta rasu a wani asibiti da ke cikin jihar.
A fadar Sarkin Kano da ke Ƙofar Kudu aka gudanar da jana’izar marigayigar mai shekara 93 salla, kafin a binne ta daga bisani.
Mun yi takaicin yadda muka rasa kujerar gwamnan kano – APC
‘Yar marigayiyar, kuma tsohuwar kwamishiniya a jihar Kano, Hajiya Zainab Audu Baƙo ce ta tabbatar da mutuwar cikin alhani lokacin zantawa da BBC Hausa ta wayar tarho.
Gwamnatin Nijeriya ta sanar da ranakun Juma’a da Litinin a matsayin hutun Easter
Mijin marigayiyar, Kwamishinan ‘Yan sanda, Audu Baƙo ya jagoranci Kano a matsayin gwamna daga 1967 zuwa 1975.
Ya shahara a matsayin ɗaya daga cikin gwamnonin Kano da suka fi aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa a jihar.

Manyan mutane daga rukunoni daban-daban ne suka halasci jana’izar matugayiya ladi Bako.