Daga Sani Idris Maiwaya
Zaɓaɓɓen Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya shawarci bankuna da masu bada bashi ko lamuni na gida da na ƙasashen ƙetare da su kauce wa bai wa Gwamnati mai barin gado bashi a wannan lokacin.
Abba ya zargi cewa Gwamnati mai ci ta ciyo basussuka da dama domin gadawar Gwamnati mai zuwa.
Mai magana da yawun zaɓaɓɓen Gwamnan Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikowa kadaura24.
Yace duk wani bashi ko lamuni da gwamnati mai ci ta karba daga bayan zabe zuwa yau, gwamnati mai jiran gado bata biya shi ba matuƙar ba’a sanar da zaɓaɓɓen gwamnan ba .
“Mun ɗauki wannan matakin ne domin shi ne bukatar al’umma Kuma zamu tsaya akan sa don kare kima da hakkin al’ummar jihar kano”.
Sanarwar ta Kuma tabbatar da cewa gwamnati mai jiran gado zata bibiyi duk wasu sharudda da gwamnati mai barin gado ta bi wajen karbo bashi daga Masu bada bashi da lamunni na gida dana kasashen waje.