Daga Halima Musa Sabaru
Hukumar kiyaye haɗura reshen jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutum biyar da suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota a kan babbar hanyar Bauchi zuwa Jos kusa da ƙauyen Panshanu.
Hukumar ta ce hatsarin ya faru ne da sanyin safiyar jiya Laraba bayan da wata mota ƙirar Toyota ta gamu da ta Peugeot waɗanda duka ke ɗauke da fasinjoji a cikinsu bayan da motar ta kuɓcewa ɗaya daga cikin direbobin.
DSS ta ce ta gano makarkashiyar kafa gwamnatin rikon kwarya a Nigeria
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa maza biyar da ke cikin motar duk sun mutu bayan da suka ƙone kurmus saboda kama da wuta da motocin suka yi.
An mika gawarwakin mutanen tare kuma da motcin zuwa hannun hukumar ƴan sanda shiyyar Toro da ke jihar ta Bauchi.
Yanzu-Yanzu: Nasiru Gawuna ya taya Abba Gida-gida Murnar lashe zaɓen gwamnan Kano
Haka-nan ma a jihar Kebbi, mutum 35 ne suka rasa rayukansu a ranar Laraba a wasu haɗura biyu da suka afku tsakanin 26-27 ga watan Maris, a cewar hukumar kiyaye haɗura a jihar.
Babban kwamandan hukumar a jihar, Yusuf Haruna Aliyu, ya ce an samu nasarar ceto mutum 40 daga haɗarin. Ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin wasu motoci guda uku waɗanda ke ɗauke da mutum 75 a cikinsu.
Ya ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti a Jega da kuma Kalgo.