Kar a kira ni da ‘His Excellency” sai bayan na bar mulki – Zaɓaɓɓen ɗan takarar gwamnan Katsina

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗa, ya bayyana dalilin da ya sa ya ce ba ya so a riƙa kiran sa “His Excellency” idan aka rantsar da shi ya kama mulkin Katsina a ranar 29 Ga Mayu.

 

Ya ce zai fi so a riƙa kiran sa da “Mr Governor ko kuma Malam Dikko Raɗɗa” amma ba ya so a riƙa kiran sa da “His Excellency”, har sai bayan ya kammala wa’adin sa tukunna.

Sake duba sakamakon zaben gwamnan Kano, APC ta bukaci ‘yan’yan ta su zauna lafiya

 

Premium Times Hausa ta rawaito cewa Raɗɗa ya bayyana haka a ranar Asabar a Abuja, lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai.

 

An zaɓi Raɗɗa a ƙarƙashin APC, ya samu ƙuri’u 859,892, ya doke Yakubu Lado na PDP, wanda ya samu ƙuri’u 486,620.

Abba Gida-gida na gayyatar al’ummar Kano zuwa shaida karɓar Shaidar lashe zabe

 

“Ni dai ba na so idan an rantsar da ni a riƙa kira na “His Excellency”, saboda kalma ce mai nuna gwamna ya cika komai, ya yi dukkan abin da ya wajaba da wanda ya kamata ya yi, da kuma nauyin da ya wajaba ya sauke.

 

“Amma idan za a iya kira na da His Excellency ɗin bayan na kammala wa’adi na, idan har jama’a sun ga na yi masu ayyuka masu kyau. Don haka ma har gara a riƙa kira na Mr Gobernor ya fi min sauƙi.

Buhari ya kaddamar da hakar Rijiyar man fetur a Nasarawa

 

“Ni ina so na ji ni ina daidai da kowa, saboda ba na son ana ƙaƙaba min ‘Excellency’ ɗin nan har ana kumbura min kai. Ni zan ma fi so kawai a riƙa kira na Malam Dikko Raɗɗa.”

Idan an tuna, a 2019 ma Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas ya cire “His Excellency” a sunan sa. Haka shi ma tsohon Gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, wanda ya yi mulki daga 2010 zuwa 2018, an riƙa kiran sa da “Ogbeni”, maimakon “His Excellency”.

Shi kuwa Gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo, ana masa laƙabi da “Arakunrin”, wato Mister kenan da kalmar Yarabanci.

Da ya ke magana kan ajandar gwamnatin sa, Raɗɗa ya ce idan aka rantsar da shi, zai fi maida hankali ne kan matsalar tsaro wadda ta addabi Jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...