Daga Rukayya Abdullahi Maida
Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da magoya bayanta da su kwantar da hankulansu su kasance masu bin doka da oda bayan bayyana sakamakon sake duba sakamakon zaben gwamna da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Kwamishinan yada labarai na jihar kano, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata.
Karamar hukumar Garum Malam ta ɗauki sabbin malaman makaranta aiki
Ya ce jam’iyyar za ta yi duk mai yiwuwa a cikin tanadin doka da sauran hanyoyin da suka dace domin ganin an yi adalci a lamarin.
INEC ta saka ranar ƙarasa zaɓukan da ba a kammala ba
Sanarwar ta bayyana cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da mataimakinsa Kuma dan takarar gwamnan Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa a takara sun bayyana gamsuwarsu da yadda ‘yan jam’iyyar ke gudanar da harkokin su kafin zabe, lokacin da kuma bayan zabe.