Daga Sani Idris Maiwaya
Zababben Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida Gida yana gayyatar dumbin magoya bayansa, yan jam’iyyar NNPP da kuma manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar zuwa karbar takardar shaidar cin zabe tare dukkan ‘yan takarar da suka ci zabe a ranar Asabar 18 ga wata.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a Kano ta tsayar da ranar Laraba 29 ga Maris, 2023 da karfe 10 na safe a matsayin ranar da zata baiwa zaɓaɓɓen gwamnan kano Shaidar lashe zabe, wanda za a yi a sakatariyar INEC ta jihar kano .
Sake duba sakamakon zaben gwamnan Kano, APC ta bukaci yan’yan ta su zauna lafiya
Mai magana da yawun zababben gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikowa kadaura24 a ranar Talata, Inda ya ce za a gudanar da taron ne a dakin taro na INEC da karfe 10:00 na safe.
Karamar hukumar Garum Malam ta ɗauki sabbin malaman makaranta aiki
Ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyar NNPP da duk mahalarta taron, da su kasancewa cikin nutsuwa da zaman lafiya da bin doka da oda, sanann ya bukace su da su gudanar da harkokinsu cikin tsari a lokacin bikin da kuma bayan bikin, tare da yi wa kowa fatan alheri.