Daga Maryam Ibrahim Zawaciki
Shahararren mawakin nan Dauda Kahutu Rarara ya ce, duk da shi ya tsayar da Sha’aban Ibrahim Sharaɗa takarar Gwamna, amma ya ɗauka da gaske yake kafin daga bisani ya gano ta wasa ce.
Rarara ya bayyana hakan hira da Jaridar Intanet ta DCL Hausa inda ya zargi Sha’aban da shinshinar PDP a zaɓen Shugaban ƙasa da ya gabata maimakon APC da suka yi yarjejeniya.
” Ni na tsayar da Sha’aban takarar gwamnan na yake yi, ya zo ya same yace yana so yayi takarar gwamnan Kano kuma gashi duk jam’iyyun sun tsayar da yan takara, ni da wasu mutane da ba sai na fadi sunansu mu muka je muka Nemo masa jam’iyyar ADP domin yayi takara a cikin ta, don haka duk wata maganar takarar Sha’aban ni nasan ta Kuma na bar shi ne saboda na fahimci ba takarar gaske yake ba”. Inji Rarara
Karanta: NNPP ta kori mataimakin dan takarar gwamna, da wasu daga cikin Shugabannin Jam’iyyar
” A cikin Mutane dubu daya da suke tare da Sha’aban dari bakwai ni na kawo su ko kuma wadanda na kawo su suka kawo su, don haka ni na tsayar da shi takarar Kuma bar shi ne saboda na fahimci ba takarar gaske yake ba “.
A cikin hirar Rarara ya bayyana cewa Nasiru Gawuna yafi kowanne dan takarar gwamnan kano chanchanta Saboda nagartar da yake da ita da Kuma yadda ya mika lamarin takarar sa ga Allah .