2023: Idan na zama gwamnan kano Zan baiwa kananan hukumomi ‘yankin cin gashin kansu – Gawuna

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi alkawarin baiwa kananan hukumomin jihar ‘yancin cin gashin kansu idan aka zabe shi a matsayin gwamnan Kano .

 

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wanj shiri na gidan talabijin din NTA Mai suna “The Balot”.

 

“Ƙananan Hukumomi wani bangare ne na gwamnati wanda yafi kusa da jama’a wanda ke taimakawa wajen cigaban al’umma ta kowacce fuska”. Inji Gawuna

 

“A matsayina na tsohon shugaban karamar hukumar na san abin da ya shafi gudanar da mulkinta”.

 

Lokacin da nake shugaban karamar hukuma, an ba ni damar yi aiki na yadda ya kamata, Hakan ta sa muka samu nasarori da dama don haka idan aka zabe mi a matsayin Gwamna nima zan basu damar cin gashin kansu”. Gawuna ya jaddada”.

 

Ya kara da cewa shi ne wanda ya fi cancanta kuma a shirye ya ke ya zama Gwamnan Jihar Kano bayan ya yi aiki da gwamnatocin da suka gabata kuma ya samu kwarewa da dama, duk da haka ya ba da tabbacin zai dora kan aiyukan da suka samu nasara akai kuma na kaucewa kura-kuran da sukai.

 

A sanarwar da babban Sakataren yada labaran mataimakin gwamna Hassan Musa Fagge ya aikowa kadaura24, yace Gawuna ya kuma bukaci al’umma musamman Matasa da su guji tada yayin zabe da bayan zabe don inganta zaman lafiyar da ake da su a kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...