Daga Isa Ahmad Getso
Jam’iyyar NNPP reshen jihar Katsina, ta kori mataimakinta dan takarar gwamna, Muttaqa Rabe-Darma, shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Sani Liti, da wasu manyan cikin shugabannin ta a jihar.
Daraktan yada labarai na jam’iyyar NNPP, Alhaji Nasiru Usman-Kankia ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kan matakin da jam’iyyar ta dauka a ranar Juma’a a Katsina, inda ya ce an kore su ne saboda munanan ayyukan da suka yiwa jam’iyya, ciki har da amincewar jam’iyyar da Marawa dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr Dikko Radda da suka yi a ranar alhamis.
“Kamar yadda kuka riga kuka sani, wani sashe na shugabannin zartaswar jam’iyyar na jihar ya kira wani taro ba tare da izini ba a ranar Alhamis 9 ga watan Maris, matakin da suka dauka a yayin taron yayi matukar girgiza jam’iyyar.
Ban ce a zabi wani dan takarar gwamnan kano da ba Abba Gida-gida ba – Sen. Kawu Sumaila
“An gabatar da taron gaggawa da ya kunshi mambobi 19 cikin 29 domin tattauna musabbabin faruwar haramtacciyar taron da wadanda muka kora suka yi.
Zaɓen Kano: Kwamitin Zaman lafiya na Kano ya gana da Kwankwaso da Abba Gida-gida
“Duk wanda ya amince da dan takarar wata jam’iyyar siyasa za a hukunta shi kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar NNPP ya tanada, tun daga dakatarwa har zuwa kora.
“Taron namu na gaggawa ya yi nazari tare da yanke shawarar korar shugabannin da mambobin da ke da ruwa da tsaki a wannan taron da aka yi shi ba bisa ka’ida ba, bayan amincewar kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa.
“wadanda muka kora sun hadar da Alhaji Sani Liti, shugaban NNPP na jihar Katsina, Umar Jibril, sakataren jam’iyyar na jiha, Mustapha Basheer, shugaban matasa, Dauda Kurfi, shugaban shiyyar Katsina, Abdulhadi Mai-Dawa, shugaban shiyyar Funtua, Dr Sale Mashi, shugaban shiyyar Daura, mataimakin dan takarar gwamna Rabe-Darma da kuma Sen. Audu Yandoma,” a cewar Usman-Kankia.