Gobara ta kone Shaguna da dama a Kasuwar Singer dake Kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano a ranar Litinin din nan ta tabbatar da cewa gobara ta kone wasu manyan kantuna da kuma babban ginin tsohon bankin Savannah da ke kasuwar Singer a Kano.

 

Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar ta ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 02:18 na safe.

 

Karanta: Sha’aban Sharaɗa ba takarar gaske yake ba, shi yasa na bar shi – Rarara

“Mun samu kiran gaggawa da tsakar dare da misalin karfe 02:18 na safe daga wani Sai’du Hamza cewa gobara ta tashi a kasuwar da ke karamar hukumar Fagge a jihar.

“Da samun labarin, mun yi gaggawar tura jami’an mu da motar kashe gobara zuwa wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 02:22 na safe domin kashe gobarar domin kada ta shafi sauran shaguna,” inji shi.

Sai dai Abdullahi ya ce gobarar ta kone shaguna na wucin gadi da dama, ya kara da cewa har yanzu hukumar ba ta gano musabbabin faruwar lamarin da kuma adadin shagunan da

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...