Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya zababben Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu murnar lashe zaben Shugaban kasa da aka gudanar ranar Asabar 25 ga watan daya gabata.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne cikin wata wasika da ya aikawa Zababben Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu.
Cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labarai na Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24 a yammacin wannan rana ta talata.
Sanarwa tace Sarkin Kanon ya bayyana Bola Tinubu a matsayin Mai hangen nesa , duba da yadda ya ciyar da jihar legas gaba a lokacin da ya yi gwamnan jihar.
” Muna fatan zaka yi amfani da kwarewar da kake da ita iya Shugabanci wajen magance matsalolin da Nigeria take fuskanta a matsayin ka na Mai kishin al’umma da kasa baki daya”. Inji Sarkin Kano
Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma bada tabbacin zasu cigaba da yiwa zababben Shugaban kasar don ya sami nasara mulkar Nigeria cikin nasara.