Daga Isa Ahmad Getso
A ranar Laraba ne wata kotun majistare da ke Kano ta tasa keyar shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta kasa Alhassan Ado Doguwa zuwa gidan yari har zuwa lokacin da ake neman belinsa.
Β Wanda ake tuhuma, Alhassan Doguwa yana fuskantar shariβa ne akan laifuffuka da dama da suka hada da, zargin hada baki, kisan kai, mallakar bindiga ba bisa kaβida ba, ta da hankalin al’umma da dai sauran su.
Β Babban Alkalin Kotun, Ibrahim Mansur Yola ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara har zuwa ranar 7 ga Maris, 2023 don sauraron bukatar neman belin.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa jami’an tsaro sun kama Alhassan Ado Doguwa a filin jirgin sama na Malam Aminu kano akan hanyar sa ta tafiya kasar saudiyya domin gudanar da ibadar umarah .