Da dumi-dumi: Kotu ta aike da Alhassan Ado Doguwa gidan yari

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

A ranar Laraba ne wata kotun majistare da ke Kano ta tasa keyar shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta kasa Alhassan Ado Doguwa zuwa gidan yari har zuwa lokacin da ake neman belinsa.

 Wanda ake tuhuma, Alhassan Doguwa yana fuskantar shari’a ne akan laifuffuka da dama da suka hada da, zargin hada baki, kisan kai, mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba, ta da hankalin al’umma da dai sauran su.
 Babban Alkalin Kotun, Ibrahim Mansur Yola ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara har zuwa ranar 7 ga Maris, 2023 don sauraron bukatar neman belin.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa jami’an tsaro sun kama Alhassan Ado Doguwa a filin jirgin sama na Malam Aminu kano akan hanyar sa ta tafiya kasar saudiyya domin gudanar da ibadar umarah .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...