Daga Auwalu Alhassan Kademi
Babban Sufeton ‘Yan sandan Najeriya ya ba da umarnin taƙaita zirga-zirgar duk wani nau’in abin hawa a kan tituna da ruwa da sauran hanyoyin sufurin ƙasar tun daga karfe 12 na daren jajiberen zaɓe.
Usman Alƙali Baba, ya ce an ɗauki matakin ne don tabbatar da yanayi mai inganci, tsaro da aminci ga harkokin zaɓen da za a yi a faɗin ƙasar.
Sanarwar ta kuma yi matsananci gargaɗi ga dukkan jami’an tsaro su guji raka mutanen da suke karewa da ‘yan siyasa rumfunan zaɓe.
Sanarwar ta ce umarnin taƙaita zirga-zirgar, na da nufin tabbatar da yanayin kwanciyar hankali da aminci ga masu zaɓe.
Akawai kuma batun taimaka wa hukumomi samar da ingantaccen tsaron rayuka da kuma hana zauna-gari-banza da masu niyyar aikata laifi zuwa su hargitsa harkokin zaɓe.
Gargaɗi
Sanarwar ta kuma ambato Babban Sufeton ‘Yan sandan Najeriya Usman Alƙali Baba yana gargaɗin duk jami’an tsaro su guji raka iyayen gidansu da ‘yan siyasa rumfunan zaɓe da cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe don kuwa duk wanda aka kama ya saɓa wa umarnin zai fuskanci hukunci mai zafi.
Sai dai sanarwar ta ce hanin da aka yi kan zirga-zirgar ababen hawan bai shafi ayyukan da suka zama tilas ba kamar sufurin jami’an zaɓe da masu sa-ido da motocin ɗaukar marasa lafiya da jami’an kashe gobara.
Usman Alƙali ya kuma jaddada cewa jami’an tsaron da kawai aka tura su ayyukan zaɓe ne ake son gani a ciki da kewayen cibiyoyi da rumfunan zaɓe.
Tunasarwa
Sanarwar ta kuma ce har yanzu haramcin amfani da jiniya ga mutanen da ba su izini da fitilun jiniya da rufaffiyar lambar mota da motoci masu duhun gilasai yana nan daram.
Haka zalika, an hana duk jami’ai masu kayan sarki na jihohi da makamantansu shiga harkokin tsaro a lokacin zaɓe.
Da yake haƙurƙurtar da ‘yan ƙasa masu kyakkyawar niyya game da rashin jin daɗin da wannan mataki zai janyo, Babban Sufeton ‘Yan sandan ya kuma buƙaci duk masu rijistar zaɓe su kasance masu bin doka kuma su fita su yi amfani da ‘yancinsu na kaɗa ƙuri’a a jibi Asabar.
Ya kuma gargaɗe su, su guji sayen ƙuri’a ko sayarwa da kalaman ƙiyayya da yaɗa labarai marasa sahihanci da kuma labaran bogi da satar akwati da sauran ayyukan laifuka.