Zan kara kyautata rayuwar ma’aikata da yan fansho idan na zama gwamnan kano – Gawuna

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Dan takarar gwamnan jihar kano a jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi alkawarin kara kuautata rayuwar ma’aikata da yan fansho na jihar kano idan ya zama gwamna a zaben dake tafe.

 

Dr. Gawuna ya bayyana hakan ne yayin da ya wakilci gwamna Ganduje wajen tarbar kungiyar yan ƙwadago ta jiha kano wadanda suka je Gidan gwamnatin jiha domin yiwa gwamnan godiya game da karin shekarun aiki da gwamnan ya yiwa ma’aikatan jihar kano.

 

Yace yana da tsare-tsare Masu yawo wadanda zasu inganta rayuwar ma’aikata da yan fansho fiye da yadda gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta yi, ta hanyar yiwa ma’aikatan karin girma akan lokaci da bada hakkokin su musamman ga wadanda suka kammala aiki.

Talla

” Nima dan ƙwadago ne Kuma Dani Akai duk wadannan aiyukan da koka zo domin yiwa gwamna Ganduje godiya, Ina baku tabbacin idan Allah ya bani gwamnan kano zan Kara fito da wasu tsare-tsaren da zasu Kara inganta harkokin aikin gwamnati da kuma tabbatar da biyan hakkokin yan fansho akan lokaci”. Inji Dr. Nasiru Gawuna

Talla daukar nauyi Hon. Surajo Umar Wudil

Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yabawa ma’aikatan jihar kano a madadin gwamna Ganduje saboda irin hadin kai da goyon bayan da suka baiwa gwamnatin tun daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

 

Da yake nasa jawabin tun da fari mai rikon mukamin Shugaban kungiyar ƙwadago ta kasa reshen jihar Kano Kwamarat Salisu Ado Riruwai ya ce sun je gidan gwamnatin ne domin yabawa gwamna Ganduje saboda amincewar da yayi har aka kara musu Shekarun kammala aiki.

 

 

Kwamarat Salisu Ado ya kuma bukaci gwamnatin da ta taimaka wajen biyan kason da ya kamata gwamnatin jihar ta biya asusun amintattu na yan fansho domin biyan hakkokin wadanda suka kammala aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...