Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya bayar da umarnin a fitar da Naira miliyan 300 don sayo magunguna da sauran kayayyakin jinya ga asibitocin gwamnatin jiha domin rabawa ga marasa lafiya kyauta wadanda akasarinsu ke fuskantar matsalar biyan kudi sakamakon karancin kudi a hannun al’umma saboda sabon tsarin CBN.
Kwamishinan lafiya na jihar Farfesa Mohammed Arab ne ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da magungunan a Maiduguri.


Arab ya ce kayyakin sun hada da magunguna na cututtuka masu yaduwa, kayan haihuwa da sauran kayan kula da marasa Lafiya.
Kwamishinan ya umurci daraktocin kiwon lafiya da manyan jami’an kiwon lafiya na cibiyoyin kula da lafiya na jama’a da ke Maiduguri da karamar hukumar Jere da su shirya don karbar kasonsu domin a gaggauta tura magungunan da sauran kayayyakin.
Arab ya ce dole ne a ba da magungunan kyauta ga marasa lafiya da ba su da kuɗi a hannu ko kuma waɗanda ke da matsala wajen samun kuɗin su don biya musu bukatunsu.